17 Agusta 2021 - 14:37
Nasrallah: Za Mu Shigo Da Makamashi Daga Iran Don Kawo Karshen Karancinsa A Labanon

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa tabbas za su shigo da makamashi da kuma man fetur daga kasar Iran, ganin har yanzu ana samun karancinsa a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Tashar talabijinn ta Al-Manar mallakin kungiyar ta nakalto shugaban yana fadar haka a zaman makokin Ashura a jiya da yamma. A wani bangare na jawabinsa Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa albarkacin sadaukarwan da yayan kungiyarsa suka yi a yakin shekara ta 2006 ne, haramtacciyar kasar Isra’ila ta kasa kaiwa kasar Lebanon hari har na tsawon shekaru 15 a halin yanzu.

Daga karshe dangane mummunan hali na tattalin arziki da tsaron da kasar take fama da su, shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ce ya zama wajibi a kan dukkan ‘yan siyasar kasar su taimaka don ganin an kafa gwammati wacce zata fitar da kasar daga wannan halin da take ciki.

342/